Sinopsis
Shiri ne na musamman, da kan tattaunawa da bangarori daban-daban na Alumma da ke sauraren Shirye shiryen RFI Hausa daga kowane kusurwa na fadin duniya, kan muhimman batutuwa, da suka shafi siyasa Tattalinariziki, aladu da dai sauransu
Episodios
-
Halin da wasu ƴan Najeriya suka shiga bayan da kamfanin CBEX ya tsere da kudadensu
17/04/2025 Duración: 09minShirin ra'ayoyin masu saurare na wannan mako ya mayar da hankali ne kan yadda wani kamfanin hada-hadar kudi ta Internet a Najeriya mai suna CBEX ya tsere da kudaden jama'a. Danna alamar sauarre domin jin cikakken shirin tare da Nasiru Sani
-
Yadda ƴan Najeriya suka shiga halin fargaba a game da yiwuwar ambaliyar ruwa a jihohi 30
16/04/2025 Duración: 10minShirin ra'ayoyin masu saurare na wannan mako ya mayar da hankali ne kan gargaɗin gwamnatin Najeriya na yiwuwar samun ambaliyar ruwa a jihohi 30 a daminar bana. Danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Abida Shu'aibu.
-
Gagarin da ilimin yara mata ya shiga sakamakon ta'addanci a Najeriya
15/04/2025 Duración: 10minShirin ra'ayoyin masu saurare na wannan rana ya mayar da hankali ne kan yadda kungiyoyin ta'addanci ke kawowa ilimin yara mata tsaiko a Najeriya. Danna alamar sauarre don jin cikakken shirin tare da Nasiru Sani.
-
Ra'ayoyin masu saurare kan batutuwan da ke ci musu tuwo a ƙwarya
14/03/2025 Duración: 10minYau ta ke ranar jin ra'ayoyin ku masu saurare kan batutuwan da ke ci muku tuwo a ƙwarya, kama daga fannin siyasa, ilimi, lafiya, tattalin arziƙi da dai sauransu. Latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyi...
-
Kan yadda EFCC ta kwato Naira tiriliyan guda daga hannun ɓarayin gwamnati
11/03/2025 Duración: 09minHukumar Yaƙi da Rashawa a Najeriya EFCC, ta ce a cikin shekarar ta 2024 da ta gabata, ta yi nasarar ƙwato kusan Naira tiriliyan ɗaya daga hannun barayi da masu handame dukiyar al’umma. EFCC ta ce ko a gaban kotu ma, ta samu nasarori sama da sau dubu huɗu akan masu cin rashawa da kuma ƴan damfara cikin shekarar da ta gabata.Abin tambayar shine, ko aikin hukumar na gamsar da 'yan Najeriya?Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakakken shirin.
-
Kan yadda direbobin manyan motoci ke fuskantar kisa daga 'yan awaren Biafara
04/03/2025 Duración: 10minƘungiyar direbobin motoci a Najeriya, ta buƙaci mahukunta su ɗauki matakan kawo ƙarshen kisan da ƴan awaren Biafra ke yi wa direbobin manyan motoci a duk lokacin da suke ratsa yankin kudu maso gabashin ƙasar. Ƙungiyar ta ce an kashe mambobinta sama da 50, kuma 20 daga cikinsu an kashe su ne a shekarar 2024, sannan aka kwashe kayayyaki da kuma ƙona motocinsu.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin.
-
Ra'ayoyin masu saurare kan batutuwan da ke ci muku tuwo a ƙwarya
28/02/2025 Duración: 10minA yau Juma'a kamar yadda aka saba, masu sauraro ko kuma bibiyarmu a shafukan sada zumunta, kan aiko da saƙonnin ra'ayoyi kan batutuwa da dama, kama daga wanda ke ci musu tuwo a ƙwarya a fannoni daban-daban na rayuwa, da kuma fannin tattalin arziki, da tsaro, da lafiya, da siyasa da sauransu.
-
Ra'ayoyin masu saurare kan yawaitar masu ta'ammali da ƙwayoyi a Arewacin Najeriya
27/02/2025 Duración: 10minAƙalla 40% na mazauna yankin arewa maso yammacin Najeriya ne ka tu’ammuli da miyagun ƙwayoyi, kuma kusan 28 cikin ɗari suna zaune ne a jihar Kaduna kamar dai yadda rahoton hukumomin da yaƙi da wannan matsala ya nuna. Hakazalika, mutum 1 cikin 7 a yankin arewa maso yammacin ƙasar suna tu’ammali da miyagun ƙwayoyin a cewar rahoton.Latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin...
-
Ra'ayoyin masu saurare kan batutuwa mabanbata
21/02/2025 Duración: 09minA yau Juma'a kamar yadda aka saba, masu sauraro ko kuma bibiyarmu a shafukan sada zumunta, kan aiko da saƙonnin ra'ayoyi kan batutuwa da dama, kama daga wanda ke ci musu tuwo a ƙwarya a fannoni daban-daban na rayuwa, da kuma fannin tattalin arziki, da tsaro, da lafiya, da siyasa da sauransu. Latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin...
-
Ra'ayoyin masu saurare kan tarar da za a ci masu satar lantarki a Najeriya
20/02/2025 Duración: 09minHukumar Ƙayyade Farashin Wutatar Lantarki a Najeriya, sanar da sabon tsarin biyan tara a kan waɗanda ke satar makamashin lantarki a ƙasar. Tarar ta kama daga Naira dubu 100 zuwa dubu 300 daidai da irin salon da mutum ya yi wajen sada gidansa da wannan makamashi.
-
Ra'ayoyin masu saurare kan saukar farashin kayan abinci a Najeriya
19/02/2025 Duración: 09minHukumar Ƙididdiga ta Ƙasa a Najeriya, ta ce farashin kayan abinci ya sauka a cikin watan Janairun da ya gabata da 10% idan aka kwatanta da na wata Disamba. To waɗannan dai bayanai da hukuma ta fitar, saboda haka za mu so jin ra’ayoyinku a game da wannan rahoto.Latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin tare da Abida Shu'abu Baraza...
-
Ra'ayoyin masu saurare kan kashe maƙudan kuɗaɗe don inganta lantarki a Najeriya
18/02/2025 Duración: 10minAlƙalumma na nuni da cewa a cikin shekaru 10 da suka gabata, an kashe aƙalla Naira Tiriliyan 7 da bilyan 200 a matsayin tallafi da nufin inganta sanar da wutar lantarki a Najeriya. To sai dai a zahirin ana cewa har yanzu wannan ɓangare na ci gaba fama da matsaloli masu tarin yawa, yayin da a ɗaya ɓangare farashin wutar ya ninka ninkin ba ninkin.
-
Ra'ayoyin masu saurare kan batutuwa mabanbanta
07/02/2025 Duración: 11minA yau Juma'a kamar yadda aka saba, masu sauraro ko kuma bibiyarmu a shafukan sada zumunta, kan aiko da saƙonnin ra'ayoyi kan batutuwa da dama, kama daga wanda ke ci musu tuwo a ƙwarya a fannoni daban-daban na rayuwa, da kuma fannin tattalin arziki, da tsaro, da lafiya, da siyasa da sauransu. Latsa alamar sauti domin sauraren ra'ayoyi mabanbanta...
-
Shirin ra'ayoyin ku masu sauraro a yau.
03/02/2025 Duración: 09mina yau shirin namu na ra'ayoyin ku masu sauraro ya yi dubu ne akan Shin ko menene ra'ayin ku a game da batun tattaunawa da 'yan bindiga.
-
Ra'ayoyin masu saurare kan batutuwa mabanbanta
31/01/2025 Duración: 09minA yau juma'a kamar yadda aka saba kuna aiko mana da saƙonnin ra'ayoyinku kan abubuwan da ke ci muku tuwo a ƙwarya a fannoni daban-daban na rayuwa, kama daga fannin tattalin arziki, tsaro, lafiya, siyasa da sauransu. Latsa alamar sauti domin sauraren ra'ayoyi mabanbanta...
-
Ra'ayoyin masu saurare kan shirin samar da lantarki ga gidaje 300M a Afirka
30/01/2025 Duración: 09minShugaban Najeriya Bola Tinubu ya sake jaddada aniyarsa ta inganta samar da wutar lantarki a faɗin ƙasar. Tinubu ya bayyana haka ne wajen taron ƙasashen Afirka wanda ya mayar da hankali akan yadda za a samar wa aƙalla mutane miliyan 300 wutar lantarki a nahiyar baki ɗaya. Latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin...
-
Ra'ayoyin masu saurare kan cikar wa'adin ficewar ƙasashen AES daga ECOWAS
29/01/2025 Duración: 09minYau 29 ga watan Janairu wa’adin farko da kasashen Nijar da Mali da Burkina Faso suka bayar na ficewa daga kungiyar ECOWAS ya cika, abinda ke tabbatar da raba garin bangarorin biyu dangane da cikar wannan wa’adi, Latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyi...
-
Ra'ayoyin masu saurare kan batutuwa mabanbanta
24/01/2025 Duración: 10minA yau juma'a kamar yadda aka saba kuna aiko mana da saƙonnin ra'ayoyinku kan abubuwan da ke ci muku tuwo a ƙwarya a fannoni daban-daban na rayuwa, kama daga fannin tattalin arziki, tsaro, lafiya, siyasa da sauransu. Latsa alamar sauti domin sauraren ra'ayoyi mabanbanta...
-
Yadda aka fara samun saukin farashin kayayyakin abinci a Najeriya
23/01/2025 Duración: 10minRahotanni daga wasu sassan Najeriya ciki har da babbar kasuwar kayan abinci dangin hatsi ta Dawanau da ke Kano na cewa an fara samun sauƙin farashin kayayyakin abincin, idan aka kwatanta da yadda al’amarin yake a watannin baya. Lamarin dai ya haifar da muhawara akan dalillan da suka janyo saukin farashin kayana abincin da ɗorewar hakan.Abin tambayar shine, ko al'umma sun gamsu da wannan rahoto, ko kuma har yanzu anan nan a gidan jiya?Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin.
-
Ra'ayoyin masu saurare kan ficewar Amurka daga WHO
22/01/2025 Duración: 09minA ƙasar Amurka, bayan rantsar da shi a matsayin sabon shugaba ƙasa na 47, Donald Trump, ya rattaba hannu kan wasu gomman dokokin zartawa na ikon shugaban ƙasa, ciki har da janye ƙasarsa daga Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), kamar yadda ya yi a wa’adin mulkinsa na farko, kafin magabacinsa Joe Biden ya maido da ƙasar ciki. Wasu na ganin wannan mataki zai yi illa ƙwarai ga ɗorewar hukumar wajen gudanar da ayyukan ta a duniya, duba da kaso mai tsoka da Amurka ke bayarwa wajen gudanar da ayyukan WHO ɗin.Latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyi...

Únete Ahora
- Acceso ilimitado a todo el contenido de la plataforma.
- Más de 30 mil títulos, incluidos audiolibros, podcasts, series y documentales.
- Narración de audiolibros por profesionales, incluidos actores, locutores e incluso los propios autores.