Tattaunawa Da Ra'ayin Masu Saurare

  • Autor: Vários
  • Narrador: Vários
  • Editor: Podcast
  • Duración: 3:57:15
  • Mas informaciones

Informações:

Sinopsis

Shiri ne na musamman, da kan tattaunawa da bangarori daban-daban na Alumma da ke sauraren Shirye shiryen RFI Hausa daga kowane kusurwa na fadin duniya, kan muhimman batutuwa, da suka shafi siyasa Tattalinariziki, aladu da dai sauransu

Episodios

  • Ra'ayoyin masu saurare game da dambarwar ƙungiyar PENGASSAN da Ɗangote

    30/09/2025 Duración: 09min

    A Najeriya ana ci gaba da kai ruwa rana tsakanin matatar Dangote da kungiyar manyan ma’aikatan man fetur da iskar gas wato PENGASSAN. Tun daga lokacin da matatar Dangote ta fara aiki kawo yanzu, an samu takaddama irir-iri daga kungiyoyin da ke da alaka da man fetur da kuma iskar gas. Ko me yasa takun saka tsakanin Dangote da masu ruwa da tsaki a harkar mai, yaki ci yaki cinyewa? Me ku ke ganin ummul aba’isin wannan dambarwa da take bullowa daga kusurwa-kusurwa, wanda ake ganin zai haifar da tashin farashin mai a Najeriya? Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku a kai........ Ku latsa alamar sauti don sauraren ra'ayoyin na ku.....................

  • Ra'ayoyin masu saurare game da yaƙin neman zaɓen Kamaru

    29/09/2025 Duración: 10min

    An ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen shugabancin ƙasar Kamaru, inda mutane 12 ciki har da shugaba mai-ci Paul Biya za su kara da juna a ranar 12 ga watan gobe na Oktoba idan Allah ya kai mu. Yayin da Paul Biya ke fatan sake samun yardar al’umma don ci gaba da mulki karo 8, a nasu ɓangare kuwa 'yan adawa na kallon zaɓen a matsayin wata dama don samar da sauyi a ƙasar. Shin me za ku ce a game da wannan yaƙin neman zabe? Ko wane fata ku ke yi wa al’ummar Kamaru? Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku akai. Latsa alamar sauti domin sauraren shirin....

  • Ra'ayoyi kan shirin Amurka na hana ƴan Najeriya masu rashawa shiga ƙasar

    25/09/2025 Duración: 09min

    Shirin Ra'ayoyin mai Saurare na wannan ranar Alhamis 25 ga watan Satumbar 2025, wanda Oumar Sani ya gabatar, ya tattauna ne kan matakin gwamnatin Amurka na hana duk wani ɗan Najeriya ciki har da jami’an gwamnati da aka samu da hannu da rashawa bisar da za ta ba su damar shiga ƙasar.

  • Ra'ayoyin masu saurare kan ficewar ƙasashen AES daga kotun ICC

    24/09/2025 Duración: 10min

    Burkina Faso, Mali da kuma Nijar sun sanar da janyewa daga Kotun Hukunta Laifuka ta Duniya da ke birnin Hague, bisa zargin kotun da kasancewa ƴar amshin ƴan mulkin mallaka. To sai dai wasu na ganin cewa shugabannin ƙasashen uku sun ɗauki matakin ne don kauce wa bincike ko tuhuma daga wannan kotu. Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacinku a yau cikin shirin na Ra'ayoyinku masu saurare. Latsa alamar sauti domin sauraren shirin...

página 2 de 2