Bakonmu A Yau

  • Autor: Vários
  • Narrador: Vários
  • Editor: Podcast
  • Duración: 1:18:11
  • Mas informaciones

Informações:

Sinopsis

A kullum mukan gayyaci masana a fannoni daban daban domin tattauna wasu muhimman al'amurra da suka shafi kanun labarai a duniya. wani lokacin kuma wasu manyan jami'an gwamnati da masu fada aji sukan kawo muna ziyara domin tattauna batutuwan da suka shafi matsalolin da suka shafe su ko kuma ci gaban kasa.

Episodios

  • Dakta Harbau akan yawan iskar gas da Najeriya ta fitar

    23/04/2026 Duración: 03min

    Wasu alƙaluma daga Hukumar Kula da Albarkatun Man Fetur na kan tudu da na cikin ruwa (NMDPRA) sun nuna cewa, adadin Iskar Gas ɗin da aka fitar daga Najeriya zuwa kasuwannin ƙetare ya kai kaso 62 cikin 100, cikin watanni uku na farkon wannan shekara. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Gas ɗin ya yi ƙaranci a Najeriyar, lamarin da ke taka rawa wajen raguwar hasken lantarkin da ake samu, fannin da kasonsa aƙalla 80 cikin 100 ya dogara da arziƙin na Gas. Don jin yadda masana ke kallon lamarin da kuma mafita, Nura Ado Suleiman ya tattauna da Dakta Aminu Idris Harbau, ƙwararren kan tattalin arziki a Najeriya. Latsa alamar sauti don sauraron hirar:

  • Dr Auwal Aliyu kan yarjejeniyar shimfiɗa bututun Gas tsakanin Najeriya da Morocco

    22/04/2026 Duración: 03min

    Najeriya da Morocco sun rattaba hannu kan wata yarjejeniyar shimfiɗa bututun Gas, aikin da zai laƙume kuɗin da yawansu ya kai Dala biliyan 25, kafin ƙarshen wannan shekara. Bayanai sun ce tsawon bututun Gas ɗin da za’a shimfiɗa ya kai kilomita dubu 6,900, wanda zai ratsa cikin Ruwa da Sahara, har ma ya tsallaka zuwa Turai. Kan wannan Shamsiyya Haruna ta tattauna da Dakta Abdullahi Auwal Aliyu, masanin tsaro a Najeriya, domin jin yiwuwar wannan aiki da kuma tasirin da zai yi. Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawar ta su.................

  • Tattaunawa da Dr Ruƙayya Yusuf Aliyu kan gargaɗin NBC ga kafofin yaɗa labarai

    21/04/2026 Duración: 03min

    Hukumar Kula da kafafen Yaɗa Labarai a Najeriya NBC, ta gargaɗi masu gabatar da shirye-shirye a gidajen Radio da Talabijin da su guji bayyana ra’ayoyin ƙashin kansu, su kuma kaucewa yin katsalandan cikin bayanan waɗanda suka tattaunawa da su, da kuma yaɗa duk wani saƙo da ka iya haifar da rarrabuwar kai. Tuni dai wannan mataki ya gamu da caccakar ƙungiyoyin farar hula da kuma ɓangaren ‘yan adawa a Najeriyar. Kan haka, Nura Ado Suleiman ya tattauna Dakta Ruƙayya Yusuf Aliyu, Malama a tsangayar koyar da aikin Jarida na zamani a Jami’ar Bayero da ke Kano a Najeriya. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar.

  • Tattaunawa da Dr Yahuza Getso kan yarjejeniyar tsaro tsakanin Najeriya da Turkiya

    20/04/2026 Duración: 03min

    Najeriya da kuma Turkiyya sun ƙulla yarjejeniyar tsaro a tsakaninsu, wadda a ƙarƙashinta matakin farko Najeriya za ta tura zatan sojoji 200 don samun horo na musamman a Turkiyya. Hakan dai na zuwa ne watanni kaɗan bayan da mahukuntan a birnin Abuja suka sanar da ƙulla irin wannan yarjejeniya da ke bai wa Amurka damar turo sojojinta zuwa Najeriya don yaƙi da ta’addanci? Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da masani tsaro lamurran tsaro Dr Yahuza Getso, domin jin tasa fahintar a game da yadda alaƙar tsaron za ta kasance tsakanin Najeriya da kuma Turkiyya. Ga dai zantawarsu.

  • Yadda gwamnatin Katsina ta gudanar da taron masu zuba jari a Faransa

    17/04/2026 Duración: 03min

    A ƙoƙarinta na ganin ta bunƙasa harkokin tattalin arzikinta, gwamnatin jihar Katsina ta ce ƙofofinta a buɗe suke ga masu  zuba jari na ƙasashen ƙetare. A yayin wani taro na masu zuba jari da ya gudana a birnin Paris na Faransa, gwamnatin jihar Katsina ta ce akwai masu zuba jarin da suka nuna sha’awar zuba jari a ɓangaren noma da ma’adinai da kiwon lafiya a jihar. Domin jin irin matakan da suke ɗauka domin cimma wannan narasa, Khamis Saleh ya tattauna da mataimakin gwamnan jihar Kastina Malam Faruk Lawal Jobe. Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.

  • Farfesa Abdulƙadir Suleiman akan cika shekaru 3 da yaƙin Sudan

    16/04/2026 Duración: 03min

    Yayin da aka cika shekaru uku da fara yaƙin basasar ƙasar Sudan, Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla mutane miliyan 14 suka bar muhallansu, baya ga daruruwan da suka rasa rayukan su. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Farfesa Abdulkadir Suleiman Muhammed na Jami'ar Abuja, kuma ga yadda zantawar su ta gudana a kai.

  • Yadda masana ke kallon zaɓen Jamhuriyar Benin

    15/04/2026 Duración: 03min

    Ɗan takarar ƙawancen jam’iyyun da ke mara wa gwamnati baya a Jamhuriyar Benin ya yi nasarar lashe 94% na ƙuri’un da aka kaɗa a zaɓen shugabancin ƙasar da aka hana fitattun ƴan adawa tsayawa takara. Romuald Wadagni mai shekaru 49 a duniya, shi ne ministan kuɗi tsawon shekaru 10 kafin shugaba mai barin gado Patrice Talon ya gabatar da shi a matsayin wanda yake son gaje shi. Don jin yadda masu sharhi kan siyasar ƙasa da ƙasa musamman a Nahiyar Afrika ke kallon zaɓen na Jamhuriyar Benin, Nura Ado Suleiman ya tattauna da Janjouna Ali Mahamane Sani.

  • Gwamnatin Najeriya ta fitar da sunayen mutane 48 da ke daukar nauyin ta'addanci

    14/04/2026 Duración: 03min

    A cikin makon nan, gwamnatin Najeriya ta fitar da jerin sunayen mutane 48 da kuma wasu kamfanoni 12, waɗanda take tuhuma da hannu cikin ayyukan ta’addanci a ƙasar. Tuni dai wannan mataki ya haifar da muhawara a tsakanin ‘yan Najeriya waɗanda ke ci gaba da tofa albarkacin bakinsu a kan lamarin. Shiga alamar sauti don sauraron cikakkiyar hira da Nura Ado Suleiman ya yi da Katfin Abdullahi Adamu Bakoji mai ritaya, masanin tsaro da ke Najeriya.

  • Abubuwan da suka haifar da saɓani a tattaunawar Amurka da Iran

    13/04/2026 Duración: 03min

    An tashi baram-baram tsakanin Amurka da Iran a tattaunawar da suka faro ranar Asabar a birnin Islamabad bisa shiga tsakanin Pakistan a ƙoƙarin kawo ƙarshen wannan yaƙi, tattaunawar da ke zuwa bayan cimma jituwar tsagaita wutar kwanaki 14 tsakanin ɓangarorin biyu. Tuni ƙasashe suka fara kiraye-kirayen ganin rashin cimma jituwar Amurkan da Iran bai taɓa yarjejeniyar da ke tsakaninsu ba Shiga alamar sauti don sauraron cikakkiyar hira da Dakta Dicko Abdourahmane malami a jami'ar Zinder Nijar....

  • Riya’uddeen Zubairu Maitama kan yarjejeniyar tsagaita wutar Amurka da Iran

    09/04/2026 Duración: 03min

    ‘Yan Sa’o’i bayan amincewa da yarjejeniyar tsagaita wutar kwanaki 14, Amurka da Iran sun zargi juna da karya yarjejeniyar, lamarin da ya kai ga Iran ta sake datse mashigin ruwan Hormuz jim kaɗan bayan buɗe shi da ta yi. Domin jin yiwuwar ɗorewar wannan yarjejeniya ta tsagaita wuta da kuma makomar ƙoƙarin da masu shiga tsakani ke yi, Nura Ado Suleiman ya tattauna da masanin Siyasar ƙasa da ƙasa, Dakta Riya’uddeen Zubairu Maitama na Jami’ar Bayero da ke Kano a Najeriya. Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawar ta su.............

  • Barista Umar Ɗanbaito kan shari'ar waɗanda ake zargi da ta'addanci a Najeriya

    08/04/2026 Duración: 03min

    Kotun musamman a Najeriya, ta ci gaba da zaman gudanar da ɗimbin shara’o’i na yanke hukunci da kuma sauraron ƙararraki kan waɗanda ake tuhuma da ayyukan ta’addanci da taimaka wa ƴan ta’addan. A daidai wannan lokaci kuma ɓangarori daban daban ke bayyana ra’ayoyinsu kan tsarin gudanar da shara’o’in lura da adadin masu laifukan da ke gurfana. Yayin da wasu ke ganin komai na tafiya daidai, wasu na ganin ana jan kafa, saɓanin taƙaita lokacin da ake buƙata.   Tu latsa alamar sauti don sauraron tattaunawar Nura Ado Suleiman da Barista Umar Usman Ɗanbaito..........

  • Comrade Musa Ayiga kan shirin Tinubu na biyan bashin lantarki na sama da Tiriliyan 3

    07/04/2026 Duración: 03min

    Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya amince da ware Naira Tiriliyan 3 da Biliyan 300 domin biyan kamfanonin rarraba wutar lantarki basukan da suke bin gwamnatin ƙasar, da zummar kawo ƙarshen matsalar ƙarancin wutar da ‘yan Najeriya ke ciki. Bayanai dai sun nuna cewa bashin na sama da Naira Tiriliyan Ukun ya taru ne a tsakanin shekarar 2015 zuwa bara. Sai dai ɗaya daga cikin masu ruwa da tsaki kan sha’anin wutar lantarki a Najeriya, Comrade Musa Yunusa Ayiga ya bayyana shakku kan wannan yunƙuri. tattaunawarsa da Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawarsu da Nura Ado Suleiman.............

  • Tattaunawa da Reverand Andrew akan bukukuwan Easter

    06/04/2026 Duración: 03min

    Ana ci gaba da gudanar da bukukuwan Easter a sassan duniya, wadda Kiristoci suka yi imani da cewa a wannan rana ce aka gicceye Yesu Almasihu inda kwanaki uku bayan hakan ya tashi. Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya tuntuɓi Reverand Andrew Doyu, domin jin ƙarin bayani a game da matsayin wannan rana da kuma muhimmancinta ga mabiya addinin Kirista. Shiga alamar sauti don saurarin cikakkiyar hirar...........

  • Intinikar Alhassan kan ƙarewar wa'adin gwamnatin Bazoum da aka hamɓarar

    02/04/2026 Duración: 03min

    A wannan rana, ta biyu ga watan Afrilun shekarar 2026 da muke, wa’adin shugabancin hamɓararen shugaban ƙasar Jamhuriyar Nijar Muhammad Bazoum ke ƙarƙarewa da a ce yana kan karagar mulki. A irin wannan ranar ce dai ta watan Afrilun shekarar 2021, aka rantsar da Mohammed Bazoum a matsayin shugaban Jamhuriyar Nijar, bayan da ya lashe sama da kashi 55 na ƙuri’un zaɓen da aka yi a watan Fabrairun wannan shekara. Akan wannan Nura Ado Suleiman ya tattauna da Intinikar Alhassan, ɗaya daga cikin makusantan hamɓararren shugaban na Nijar. Ku latsa alamar sauti don sauraren tattaunawarsu............

  • Mammane Wada kan shirin Nijar na kafa ƙungiyoyin samar da tsaro da basu makamai

    01/04/2026 Duración: 03min

    A Jamhuriyar Nijar, ra’ayoyi sun banbanta a kan shawarar da gwamnatin ƙasar ta yanke na kafa ƙungiyoyi waɗanda za ta bai wa horo tare da riƙe makamai don kare garuruwa daga hare-haren Ƴanbindiga. A cewar gwamnati, jami’an ƙungiyoyin kare kan, za su kasance sojoji, da ƴansanda da sauran jami’an tsaron da suka yi ritaya, waɗanda za a riƙa biyansu kuɗin alawus. Kan wannan Nura Ado Suleiman ya tattauna da Mammane Wada na ƙungiyar Transparency International da ke bibiyar lamurra a ƙasar ta Nijar. Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawarsu............

  • Tattaunawa akan shirin samar da ƴansandan jihohi a Najeriya

    31/03/2026 Duración: 03min

    Kwamitin da Sufeto Janar na Ƴansandan Najeriya Tunji Disu ya kafa domin bada shawarar yadda za’a kirkiro ƴansandan jihohi ya gabatar da shawarwarinsa ga kwamitin Majalisar tarayya dake yiwa kundin tsarin mulki kwaskwarima. Shugaban kwamitin Farfesa Olu Ogunsakin ya bayyana cewar sun bada shawarar mayar da kashi 60 na ƴansandan tarayya da ake da su yanzu zuwa sabuwar rundunar ƴansandan jihohin da za’a kirkiro a jihohi 36 da Abuja. Danna alamar sauti domin sauraron cikakkiyar hirar Bashir Ibrahim Idriss da Sufet Muhammed Wakili mai riyata....

  • Darusan da aka koya a kwanaki 30 na yakin Gabas ta Tsakiya

    30/03/2026 Duración: 03min

    Yayinda ake cika wata guda curr da fara yaƙi tsakanin haɗin gwiwar Amurka da Isra’ila a gefe guda kuma da Iran, a yau ɓangarorin da ke rikici na ƙara zafafa hare-hare, a wani abu da duniya ke ci gaba da mamakinsa. Zuwa yanzu dai wannan yaƙi ya laƙume dubban rayuwa, inda kuma Iran ke zargin Amurka da shirya afka mata da sojoji ta ƙasa, yayinda wasu ƙasashe suka fara yunƙurin sulhunta tsakani. Shiga alamar sauti don sauraron karin bayani a hirar da Rukayya Abba Kabara ta yi da Bash M Bash....

  • Tattaunawa da Dr Maman Kassou na jami’ar Andre Salifou a Nijar kan cinikin bayi

    26/03/2026 Duración: 03min

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana fataucin bayi da aka share ɗaruruwan shekaru ana yi daga Afirka zuwa Turai da Amurka a matsayin ‘’cin zarafin bil  Adama mafi girma’’ da aka taɓa gani a tarihi. Ƙasashen duniya 123 ne suka kaɗa ƙuri’ar goyon bayan wannan ƙuduri, wasu uku wato Amurka, Isra’ila da Argentina suka ƙi amincewa yayin da wasu ƙasashe 52 suka yi ƙememe ta hanyar rowar ƙuri’unsu. To domin tuni a game da lokacin da aka fara ɗibar bayi daga Afirka da kuma yadda hakan ya shafi ci gaban nahiryar, Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da masani tarihi Dr Maman Kassou, malami a jami’ar Andre Salifou da ke Damagaram, ga kuma zantarwarsu. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar tattaunawar.

  • Yadda rikicin Gabas ta Tsakiya ke tasiri akan farashin kayayyaki a duniya

    25/03/2026 Duración: 03min

    Farashin hajoji da sauran muhimman abubuwa na ci gaba da hauhawa a kasuwannin duniya sakamakon yadda yaƙin da ake yi a yankin Gabas ta Tsakiya ya hana fitar da mafi yawan man fetur da kamfanoni da masana’antu suka yi oda ya maƙale a Mashigin Ruwan Hormuz. To domin fahintar girman wannan matsala da kuma ɓangarorin da suka fi fama da ƙarancin makamashi a duniya saboda wannan rikici, Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya tuntuɓi masani tattalin arziki Dr Isa Abdullahi, malami a jami’ar Tarayya da ke Kashere a jihar Gomben Najeriya, ga kuma zantawarsu. A latsa alamar sauti domin sauraron tattaunawar

  • Yaƙin da ake a Iran ya ritsa da ɗimbin ƴan ƙasashen waje da ke karatu a ƙasar

    24/03/2026 Duración: 59s

    Yanzu haka yaƙin da ake fama da shi a yanzu Gabas ta Tsakiya ya rutsa da ɗimbin ƴan kasashen waje musamman ɗalibai da ke karatu a ƙasar Iran. To sai dai yayin da wasu ƙasashe suka fara kwashe mutane zuwa gida ko kuma wasu ƙasashe, amma har yanzu Najeriya ba su samu irin wannan tallafi daga gwamnatinsu ba. A game da haka ne Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Muhammad Umar Nuruddeen, ɗaya daga cikin ɗaliban ƴan Najeriya wadanda adadinsu ya zarta 500, wanda ya fara da yin bayani a game da yadda rikicin ya tarar da su Ku latsa alamar sauti da ke sama domin jin wannan tattaunawa.................................

página 1 de 2