Sinopsis
Shirin Lafiya yana tattaunawa da likitoci da mahukunta a game da kiyon lafiyar jamaa, Sanin sabbin magunguna da binciken kimiya ya samar. Ana gabatar da shirin a ranar Littinin da hantsi, tare da maimaici a ranar Talata da yamma.
Episodios
-
Asusun UNICEF ya koka kan ƙaruwar ƙananan yara da ke fama da yunwa a Najeriya
18/08/2025 Duración: 09minShirin 'Lafiya Jari Ce' a wannan mako, ya tattauna da masana da sauran masu ruwa da tsaki akan wani rahoton Asusun kula da ƙananan yara na Majlisar Ɗinkin Duniya UNICEF, wanda ya bayyana ƙaruwar adadin yaran da ke fama da yunwa ko kuma ƙarancin sinadaran abinci masu gina jiki a wasu sassan arewacin Najeriya.
-
Muhimmancin shayar da jarirai nonon uwa zallah a watannin shidan farko
11/08/2025 Duración: 10minA wannan makon shirin ya yi duba kan tsarin nan na shayar da nonon uwa zalla ga jarirai tun daga haihuwa har zuwa watanni 6 ba tare da silki ba, tsarin da ake cigaba da ganin mabanbantan ra’ayoyi hatta daga iyaye dama wasu jami’an lafiya. Bisa al’ada kowanne makon farko na watan Agusta na matsayin makon shayar da Nonon uwa zalla da ake kira Exclusive Breast Feeding a turance, da nufin ƙarfafa gwiwar iyaye wajen rungumar tsarin na shayar da Nonon Uwa zalla ga jarirai, makon da a wannan shekarar ke da taken Fifita tsarin shayar da jarirai Nono zalla don samar tallafi mai ɗorewa.
-
Matakin Amurka ka iya haifar da koma baya ga shirin yaki da cutar HIV a Najeriya
04/08/2025 Duración: 10minShirin ya mayar da hankali ne kan yadda matakin Amurka na janye tallafin da take ba wa ɓangaren kula da masu fama da cuta mai karya garkuwa jiki ta HIV da ake fargabar zai iya haifar da koma baya ga shirin yaƙi da cutar. Tuni hukumomi a duniya suka fara tofa albarkacin bakinsu kan wannan mataki da shugaban Amurka, Donald Trump ya ɗauka, wanda ake ganin zai fi yin tasiri ne ga nahiyar Afirka. Tuni mujallar Lancet ta Biritaniya ta yi hasashen cewa matakin na Donald Trump na iya haifar da mutuwar mutane sama da miliyan 14 nan da shekarar 2030, ciki har da yara sama da miliyan 4.5 'yan kasa da shekaru biyar. Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashi Aminu.
-
Yadda matsalolin tsaro ke haddasa ƙarancin abinci da ke assasa cutukan yunwa
14/07/2025 Duración: 09minShirin Lafiya Jari ce tare da Azima Bashir Aminu a wannan makon ya yi duba kan yadda matsalolin tsaro ke haddasa ƙarancin abinci wanda ke matsayin masabbabin cutuka masu alaƙa da yunwa musamman a yankunan jihohin Sokoto da Zamfara da matsalolin ƴanbindiga suka zama ruwan dare. Shirin ya tattauna da masana daga yankunan waɗanda suka bayar da shawarwari kan yadda za a tunƙari matsalolin na ƙarancin abinci dama cutukan da suke haddasawa. Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin.