Sinopsis
A kowace Litinin da Juma'a a shirye-shiryen Safe da Dare ana gabatar da Shirin Duniyar Wasanni akan batutuwa daban-daban da suka shafi wasanni a sassan duniya.
Episodios
-
Yadda aka faro kakar gasar Firimiyar Ingila ta bana
14/10/2024 Duración: 09minShirin a wannan makon ya maida hankali ke kan yadda aka faro gasar Firimiyar Ingila, inda akwa yanzu kowace ƙungiya ta samu nasarar buga wasanni 7-7. Tuni gasar ta soma nisa, inda Liverpool take a saman teburi da maki 18, yayinda Arsenal da Manchester City ke biye mata da maki, 17, kowannen su. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh......
-
Ko komen da Ahmed Musa yayi Kano Pillars zai haifar da ɗa mai ido?
07/10/2024 Duración: 09minShirin Duniyar Wasanni na wannan lokaci yayi duba ne kan komen da Kyaftin din tawagar Najeriya Ahmed Musa ya yi wa tsohon ƙungiyarsa Kano Pillars tare da abokin wasansa Shehu Abdullahi. A karshen makon da muka yi bankwana da shi ne dai ƙungiyar kwallo ƙafa ta Kano Pillars a hukumance ta sanar da kulla yarjejeniyar shekara guda da ƴan wasan. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh......
-
Matakin da Hukumar CAF ta ɗauka kan Ghana ya bar baya da ƙura
30/09/2024 Duración: 09minA dai-dai lokacin da ake ci gaba da shirye-shiyen wasannin sharen fagen samun gurbi a gasar lashe kofin Afrika, Hukumar Kula Ƙwallon kafar Afrika CAF ta ce filayen wasan ƙasar Ghana ba su da ingancin da ya kamata a ce an gudanar da manyan wasanni na kasa da kasa a cikin, matakin da ke kara nuna gazawar ƙasar. Ita dai hukumar CAF ta ce ba komai ya sanyata daukar wannan mataki ba, face yadda ta ce aƙwai rashin wadatatciyar ciyawa da rashin magudanun ruwa da dai sauransu a filin wasa na Baba Yara da ke birnin Kumasi, haka ta ce abin ya ke a sauran filayen wasanni irin na Cape Coast da kuma na Accra.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh......
-
An shiga mako na uku a gasar firmiyar Najeriya
23/09/2024 Duración: 09minShirin a wannan lokaci zai leka gasar Firimirar Najeriya wato NPFL Wanda aka shiga mako na uku da somawa.Gasar Firimiyar Najeriya na daga cikin manyan gasannin Lik-lik da ake ji da su a nahiyar Afrika, musamman idan akayi la’akari da yadda ƙungiyoyin da ke fafatawa a wannan gasa ke taka rawar gani a gasar zakarun Ƙungiyoyin Afrika.

Únete Ahora
- Acceso ilimitado a todo el contenido de la plataforma.
- Más de 30 mil títulos, incluidos audiolibros, podcasts, series y documentales.
- Narración de audiolibros por profesionales, incluidos actores, locutores e incluso los propios autores.