Lafiya Jari Ce

An fara gangamin rigakafin cutar Typhoid irinsa na farko a Jamhuriyyar Nijar

Informações:

Sinopsis

Shirin Lafiya Jari ce a wannan makon ya mayar da hankali kan gangamin rigakafin cutar Typhoid da mahukuntan Jamhuriyyar Nijar suka faro a faɗin ƙasar, irinsa na farko da aka taɓa gani a tarihi a wani yanayi da ake ganin ta’azzarar wannan cuta a ƙasar ta yankin Sahel. Wasu alƙaluman hukumar Lafiyar Jamhuriyyar Nijar a 2021 sun ce mutane dubu 30 suka kamu da cutar, a wancan lokaci wadda ta haddasa mutuwar mutane 400. Kodayake a baya-bayan nan babu cikakkun alƙaluman ta’adin cutar, sai dai matakin mahukuntan na fara wannan rigakafi ya nuna tabbacin ta’azzararta. Jihar Agadez na ɗaya daga cikin yankunan da cutar Typhoid ta fi yaɗuwa, kuma tuni aka faro wannan rigakafi da zai shafi mutanen da shekarunsu ya fara daga 1 har zuwa 19 a wani yunƙuri na daƙile yaɗuwar cutar. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu.............