Kasuwanci

Tasirin tattalin arzikin shigar sabbin kasashe kungiyar BRICS

Informações:

Sinopsis

Shirin 'Kasuwa Akai Miki Dole na wannan mako ya maida hankali ne kan taron Kungiyar BRICS ta kasashe masu tasowa wadanda suka kunshi Brazil da Rasha da India da China da kuma Afirka ta Kudu, wanda aka kafa ta domin kalubalantar kaifin tattalin arzikin kasashen yammacin duniya, wadda ta amince da shigar da sabbin kasashe shida cikinta amatsayin mambobi, wato Saudiyya da Iran da Habasha da Masar da Argentina sai kuma Hadaddiyar Daular Larabawa.